APC Annoba Ce Ga ‘Yan Najeriya – In Ji PDP

Wani tsohon dan takarar shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Raymond Dokpesi, ya ce, lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su dawo daga rakkiyar jam’iyyar APC mai mulki.

Dokpesi, ya yi wannan kira ne a Katsina a yayin da ya jagoranci wata tawagar tuntuba ta neman goyon bayan sake tsayar da tsohon shugaban kasa, Atiku Abubakar, a matsayin dan takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam’iyyar ta PDP a shekara mai zuwa.

 

Dokpesi ya ce, irin mummunar tabarbarewar da al’amuran kasar suka yi, darasi ne ga al’umma, yana mai kira da babbar murya a garesu da su canza tunani ta hanyar zaben PDP a shekarar 2023 domin daidaita al’amura da kyautata jin dadin rayuwarsu kamar dai yadda aka gani a zamanin mulkinta daga shekarar 1999 zuwa 2015.

Ya jaddada cewa, fitar da Najeriya daga mawuyacin halin da take ciki, na bukatar zakakurin shugaba, mai gogewar harkokin mulki da siyasa irin Atiku Abubakar.

Dokpesi ya bayyana cewa, tsarin mulkin PDP ne ya bayar da damar zagayawa da kujerar shugaban kasa a tsakanin kudu da arewa domin tabbatar da adalci kuma har yanzu a kan wannan tsari ake, don haka, ya dace a bai wa dan arewa dama bayan da Jonathan daga kudu ya mulki kasar a baya.

A sa’ilin da yake nasa jawabin, shugaban jam’iyyar PDP na jihar Katsina, Salisu Majigiri, ya ce, reshen jam’iyyar na jihar zai goyi bayan dukkanin matakin da za a dauka idan har zai kai jam’iyyar ga samun nasara da hadin kai a dukkanin matakai.

Sauran wadanda suka maganta a wajen taron wanda ya hado wakilan jam’iyyar daga kananan hukumomi 34 na jihar, sun hada da tsohon sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Umar Tsauri da tsohon dan takarar gwamnan jihar, Sanata Yakubu Lado da dai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram