PDP Ta Karyata Tsohon Jigonta, Fani-Kayode

Jam’iyyar PDP ta ce, ba ta kai kujerarta ta takarar shugaban kasa ta 2023 ko ina ba tukuna.

Sakataren hulda da jama’a na kasa na jam’iyyar, Debo Ologunagba, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Asabar.

PDP na maida martanin ne bayan da wani tsohon jigonta wanda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a shekarar 2021, Femi Fani-Kayode, ya yi ikirari a cikin wani shirin gidan talabijin na Channels cewa, jam’iyyar ta PDP ta rigaya ta bai wa tsohon shugaban kasa, Atiku Abubakar tikitin zama dan takararta na shugabancin kasa.

Ologunagba, wanda ya bayyana furucin na Fani-Kayode a matsayin shaci-fadi, ya ce, PDP jam’iyyace da ta ginu a kan tsarin dimokuradiyya, don haka, kafin daukar duk wani mataki, ciki har da tsarin zagayawa da kujerun takara, sai ta yi tuntuba da tattaunawa mai tsawo da dukkanin masu ruwa da tsaki domin tabbatar da hadin kai da zaman lafiya da ci gaban kasa kamar dai yadda ta saba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram