Ƴan Najeriya Za Su Ci Moriyar Turbar Da Buhari Ya Ɗora Najeriya Bayan Ya Sauka – Bashir Ahmad

Mai taimaka ma Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a kan kafafen sada zumunta na zamani, Bashir Ahmad, ya ce ƴan Najeriya ba za su ga amfanin turbar da Buhari ya ɗauka ba ta inganta ƙasar sai bayan ya bar mulki.

Bashir Ahmad, ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook a ranar Litinin ɗin nan.

“Turbar da Shugaba Buhari ya ɗauka ba za a ga amfaninta a fili ba a yanzu sai bayan ya bar mulki.

Ya ɗora ƙasar nan akan kyakykyawan tsarin da duk shugaban da ya zo zai ɗora.” In ji shi.

Ya ci gaba da cewa, wasu tsare-tsaren na gyara ba sa yiwuwa sai an sha wuya sai dai idan aka haƙura daga ƙarshe za a ci moriyarsu nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram