Ɗalibai Za Su Daina Zuwa Makaratu A Ranar Juma’a A Kaduna

Gwamnatin Kaduna da ke Arewacin Najeriya, ta umarci makarantun gwamnatin jihar da su fara aiki kwana huɗu a sati – maimakon biyar – a daidai lokacin da ake komawa makarantu a yau Litinin don ci gaba da zango na biyu na shekarar karatu ta 2021/2022.

BBC ta ce, Kwamashiniyar Ilimi a jahar Halima Lawal ce ta bayar da umarnin a Kaduna ranar Lahadi cikin wata sanarwa da kamfanin Labarai na NAN ya ruwaito.

A ranar 1 ga watan Disamba na 2021 ne gwamnatin ta Kaduna ta fara aiki da kwanakin aiki huɗu a mako.

Mai magana da yawun Gwamna Nasir El-Rufai ya ce nan gaba su ma makarantu masu zaman kansu za su fara aiki da sabon tsarin.

Kwamashiniyar ta ce za su tabbata cewa an kammala sabon zangon karatun cikin tsari ba tare da sabon tsarin ya lalata kalanda ko jadawali ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram