An Yi Garkuwa da Mutum 4 a Jihar Kogi

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutane hudu da suke dawowa daga wani bikin suna a Oko zuwa Egbe na karamar hukumar Yagba ta Yamma a jihar Kogi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 8 na dare.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an ‘yan sanda da ‘yan banga sun shiga cikin dajin a yankin domin bin sawun barayin bayan samun labarin afkuwar lamarin.

Sai dai hakar nasu bai cimma ruwa ba har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi (PPRO), ASP William Aya, bai dauki waya domin tabbatar da faruwar labarin ba.

Sai dai rahotanni daga mazauna yankin na nuni da cewa an tura wani na’uran leken asiri zuwa yankin domin gano barayin.

Wata majiya ta tabbatar da ganin wannan Na’ura na shawagi a sararin samaniyar yankin a ranar Lahadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram