Mutum 38 Sun Kamu Da Cutar Shan-In-na A Jihar Bauchi

Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Bauchi (BASPHCDA) ta ce, ta samu rahoton mutane 38 da aka tabbatar sun kamu da cutar Shan in-na wato Polio Virus Type 2 (Cmpv2) a kananan hukumomi 12 dake jihar.

Shugaban Hukumar BASPHCDA, Dokta Rilwanu Mohammed ne ya bayyana haka a Bauchi a karshen makon jiya, a lokacin da ya ke kaddamar da allurar rigakafin cutar a garin Bayan Fada.

Ya ce kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Toro, Warji, Darazo, Misau, Dambam, Zaki, Jamaare, Alkaleri, Ganjuwa, Bauchi, Katagum da Shira.

Shugaban ya ce yawan mutanen da aka yi niyyan yiwa rigakafin a lokacin aikin ya hada da Yara dake da shekaru 5 wadanda yawansu ya Kai jimillar 2,286,057 yayin da allurar rigakafin ya kai 2,367,450.

Rilwanu ya ce an gudanar da taron daidaita tsakanin iyakokin jihar Bauchi da Makwaftanta kamar su Jigawa, Kano, Yobe, Gombe, .

Ya ce WHO da UNICEF sun dauki nauyin aiwatar da dabarun DOPV a duk kananan hukumomin da ke da hatsarin gaske wajan kamuwa da cutar a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram