Shekaru 10 Da Sanya Dokar Hana Hawa Babur Buni Ya Ɗage Dokar A Yobe

Gwamnan Jahar Yobe Mai Mala Buni ya ɗage dokar dokar hana amfani da Babura a Ƙananan Hukumomin 10 na Jahar Yobe ta Yamma, da Kudu na Jahar.

Buni ya sanar da hakan a Fadar Sarkin Nguru a lokacin da yake jajanta ma ƴan ƙauyen akan gobara data faru a Kasuwar Nguru.

Buni yace yanzu mazauna Jahar suna da damar daza su yi amfani da Baburan su a gonakin su da sauran wasu ayyuka.

Ya yi nuni dacewar sabbin Matakan an ɗauke su ne domin yanayin tsaro da aka samu a yankunan.

Gwamnatin Jahar Yobe ta sanya dokar hana amfani da Babura a lokacin da faɗan Boko Haram yake kanshi a watan Janairun shekarar 2012.

Biyo bayan wannan ɗage dokar, za’a iya amfani da Babura a Al’ummomi irin su Bade, Nguru, da Karasuwa, da Yusufari, da Machina, da Jakusko, da Fune da Fika, da Nangere, gami da Karamar hukumar Potiskum.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram