Tinubu Ya Sanar Da Buhuri Ƙudirinsa Na Tsayawa Takarar Shugabanci Najeriya A 2023

Jigon Jam’iyyar APC na Ƙasa Asiwaju Bola Tinubu yace ya shaidawa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ƙudirin shi na tsayawa takarar shugabancin Najeriya.

Tinubu ya bayyana haka a tattaunawar shi da Manema labaru bayan ya yi taro da Shugaban Ƙasa a Aso Rock a ranar Litinin.

“Na sanar da Shugaban Ƙasa ƙudiri na na tsayawa takarar shugabancin Najeriya, amma ban sanar da ƴan Najeriya ba. Har yanzu ina cigaba da neman shawara,” inji shi.

Duk da cewa alamu sun tabbata cewa yana son Shugaban Ƙasa, Tinubu yana cigaba da kiyaye amsa tambaya kai tsaye akan hakan.

A yayinda Ƙungiyoyin dake goyon bayan shi a faɗin ƙasa da kuma takardu dake yawo, amma Jigon baya son magana akan haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram