Shugaba Joe Biden na Amurka ya nada wata ‘yar Najeriya, Titilayo Ebong, a matsayin Daraktar hukumar kula da ci gaban kasuwancin kasar, USTDA.
Hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwar da ke dauke da jerin sunayen mutanen da aka aike wa majalisar dokokin kasar domin nada su a kan mukamai daban daban a cikin majalisar zartaswar gwamnatin Biden din.
Rahoton da muka samu daga jaridar ‘Punch’ ya nuna cewa, Ebong, ta rike mukamai daban daban a hukumar ta USTDA a tsakanin shekarun 2004 da 2019, da suka hada da babbar mai bayar da shwarwarin shari’a da mataimakiyar darakta.
Kafin ta soma aiki da hukumar ta USTDA, Ebong, sai da ta yi aiki a matsayin lauya mai wakiltar kamfanonin gwamnati da na masu zaman kansu a birnin Boston.
Kamar yadda sanarwar ta bayyana, shugaba Biden ne ya nada Ebong din a matsayin babbar jami’ar kula da aikace-aikacen hukumar kuma mai rikon mukamin daraktar hukumar tun daga lokacin.
Ebong ta samu digirinta ne na farko daga jami’ar koyon aikin lauya ta Michigan da digiri na biyu a kan hakokin sadarwa daga kwalejin koyon aikin sadarwa ta jami’ar Pennsylvania.
Ebong, ta tashi ne a jihar Legas kuma mahaifinta, Ime James Ebong, ma’aikacin gwamnati ne wanda ya taba rike mukamin babban sakatare.