Wani Likita dake aiki da Hukumar Lafiya Ta Duniya a Jahar Benue ya mutu sakamakon zazzaɓin Lassa.
Wakilin Majiyar mu ya shaida cewa Likitan wanda aka bada sunan shi da Samuel Tagher Nyitor ya mutu a ranar Lahadi a dalilin cutar, bayan an kaishi Asibiti Ƙwararru na Jahar Edo.
Akwai kuma wani rahoto dake cewa wani mutum da likita ya yiwa magani ya mutu a satin daya wuce a Jahar, shima likitan ya killace kansa.
Amma Kwamishinan Lafiya da Cigaban Al’umma Dr Joseph Ngbea ya tabbatar wa da Manema labaru a Makurɗi a ranar Litinin cewa Likitan da aka kai a Asibitin Irrua shine ya mutu.
Ngbea wani dake fama da cutar a Asibitin Koyarwa na Jahar Benue yana nan da ransa, kuma babu wani alamun rashin lafiya.
Kafin yanzu, Gwamnan Jahar ya saki kuɗi domin bincike, kuma mun sayi maganin Naira 600,000 ga duk wanda ke fama da cutar a Asibitin.
Kwamishinan ya buƙaci mazauna Jahar dasu guji duk wani abu dazai kawo Ɓera, kuma idan suka ji suna fama da rashin lafiya suka kai kansu a Asibiti domin ɗaukar matakin gaggawa.