Karka Kuskura Kayi Aure Idan Baka Da Kudi–Ifuennada
Tauraruwar Reality TV, Uloma wacce aka fi sani da Ifuenada ta yi wa masoyanta nasiha.
Iheme ta kasance tsohuwar ƴar jaruma a Zango na Uku na Shirin Fim din “Double Wahala” Big Brother Naija a cikin shekarar 2018.
Tsohuwar ‘yar Jarumar na Big Brother Naija ta bayyana hakanne a shafinta na Instagram a ranar Lahadin da ta gabata inda ta bayyana ra’ayinta game da aure da kuma kudi kamar yadda ta rubuta, “Dan Allah kada ku yi aure idan Baku da Kudi Kuma karki haifi Yara idan kunsan Baku da Kudi, Wasu mutane suna yin waɗannan abubuwan ne saboda suna jin ɗan danginsu/abokinsu mai arziki ne, amma wannan zalunci ne, musamman ga yaran da kuke kawowa cikin wannan duniyar. Ku bar wadannan Yara tukunnan, har sai kun sami kuɗin kula da su. Ya kamata mu gyara Halayen zuwa masu kyau a wannan shekara ta 2022. ”inji ta.
Ta kuma kara da cewa, “Babu kudin banza a wannan shekarar. Idan na ba ka kuɗi, dole ne ka biyani, sai dai Dan, na yi ninyan yin kyauta ko sadaka.”