Tatsuniya Ce Babba, Batun Sha’awar Takarar Tinubu Ta Shugabancin Najeriya

Wani Jigo a Jam’iyyar PDP Chief Bode George ya bayyana batun sha’awar takarar shugabancin Jigon Jam’iyyar APC na Ƙasa Asiwaju Bola Tinubu a matsayin tatsuniya ce ta wasan yara.

George ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da Manema labaru a ranar Litinin, a sa’ilin da yake maida jawabi akan matakin Tinubu na sanar da Buhari batun tsayawar shi takara.

” Wannan sha’awar tashi ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya bata irin wanda ya dace da Bola Tinubu. Dubi yanda ya lalata dukiyar jahar Lagos. Abun mamaki ne yayi mafarkin zama Shugaban Ƙasa.

Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP yace Tinubu zaiyi mamakin yadda abubuwa zasu tafi, da kuma yadda zai faɗawa abubuwan da yayi imani a kansu.

George yace yankin Kudu maso Yamma nada nagartattun Shuwagabanni wanda zasu iya fito da Shugaban Ƙasa na gaba.Kuma Tinubu baya cikin su.

Abun cin mutunci ne ace yankin Kudu maso Yamma, wanda itace yanki mafi tsada ta fido da Tinubu.

George yace abun baƙin ciki ne yanda fadar shugaban ƙasa ta zama wurin da Tinubu zai bayyana ra’ayin shi na tsayawa takarar shugabancin Najeriya.

Tinubu wanda ya taɓa zama Gwamnan Lagos, ya shaidawa Buhari cewa zai tsaya takara a zaɓe mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram