Hukumar zabe ta jihar Katsina, SIEC, ta bayar da sanarwar cewa, za a gudanar da zaben kananan hukumomin jihar a ranar 11 ga watan Afrilu na wannan shekara ta 2022.
Sanarwar ta fito ne daga bakin shugaban hukumar, Ibrahim Bako, a lokacin wani taron ‘yan jaridu da ya gudana a ofishinsa a ranar Talata.
Bako, wanda ya taya al’ummar jihar Katsina farin ciki dangane da hakan, ya ce, doka ce ta hana gudanar da zaben a can baya a sabili da karar da shugabannin kananan hukumomin da aka dakatar suka kai gwamnatin jihar.
Ya ce, shari’ar ta kwashe kimanin shekaru 5 ana yinta tun daga kasa har zuwa kotun koli wadda ta gabatar da hukuncin karshe a shekarar da ta gabata, wanda kuma shine a yanzu ya bayar da damar yin zaben.
Shugaban na SIEC ya kara da cewa, sanarwar, dama ce ga jam’iyyun siyasa su soma shirye-shiryen tsayar da ‘yan takara tare da yakin neman zabe daga yanzu zuwa jajiberin zaben wato 10 ga watan Afrilu.
Bako ya kuma roki hadin kai da goyon bayan al’umma da jam’iyyu da sauran masu ruwa da tsaki, yana mai cewa, an yi dukkanin shirye-shiryen da suka kamata wajen ganin zaben ya gudana cikin nasara.
Taron ya samu halartar wakilan jam’iyyu da hukumar zabe ta kasa, INEC, da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.