An Kama Sojojin Burkina Faso 8, Kan Shirin Hargitsa Cibiyoyin Sojin Kasar

An tsare sojoji takwas ciki har da wani babban kwamanda saboda shirin zargin Shirin “Tada Hargitsi” a cibiyoyin Soji na kasar Burkina Faso, kamar yadda masu gabatar da kara na soji da majiyoyin tsaro suka bayyana a jiya Talata.

Ofishin mai shigar da kara na soji a Ouagadougou babban birnin kasar ya ce ya samu labarin “zargin wani aiki na hargitsa cibiyoyin jamhuriyar da wasu gungun sojoji ke shirin yi”.

Ofishin ya ce, ya samu labarin shirin ne a ranar Asabar bayan “wani dan kungiyar da suka shirya lamarin” ya yi Tona asirin shirin, in ji sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa an fara gudanar da bincike tare da tsare sojoji takwas domin yi musu tambayoyi.

Gwamnatin kasar Afirka ta Yamma ta fuskanci matsin lamba kan gazawarta wajen dakile zubar da jinin, a wani kazamin fadan tsakanin Gwamnatin kasar da Masu ikirarin jihadi na tsawon shekaru shida wanda ya lakume rayukan mutane kusan 2,000 tare da tilastawa mutane miliyan 1.4 barin gidajensu.

Majiyoyin tsaro sun shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, Laftanar Kanar Emmanuel Zoungrana, kwamandan sojojin yammacin kasar da ke yaki da masu jihadi a kasar na cikin wadanda aka kama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram