Ana Ci Gaba Da Aikin Ceton Masu Ibada Da Suka Makale A Ginin Cocin Delta

Ana ci gaba da aikin ceto a Cocin Ministry Salvation da ke Okpanam, a karamar hukumar Oshimili ta Arewa a jihar Delta, inda wasu masu ibada suka makale bayan Ruftawar Ginin Majami’ar.

Ginin cocin, wanda aka fara amfani da shi a karon farko, ya fado ne a yayin da ake gudanar da ibada da misalin karfe 6 na yammacin jiya Talata, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 10.

Mutane na ci gaba da neman ‘yan uwansu a wurin da lamarin ya faru a yau Laraba.

An kuma ce wasu masu ibada da dama sun makale a baraguzan Ginin Cocin da ya Rufta, Amma an ceto mutum takwas sannan an kai mutane hudu zuwa Asibitin kwararru na Asaba.

Wakilin Majiyar Jaridar Jakadiya ta rawaito cewa sama da mutane 30 ne aka ceto ba tare da sunji rauni ba, sa’o’i kadan bayan rugujewar Ginin.

Sakataren gwamnatin jihar, Cif Patrick Ukah, kwamishinan lafiya na jihar, Dr Ononye Mordi, da tawagar jami’an kungiyar agaji ta Red Cross da ‘yan kwana-kwana na wurin da lamarin ya faru, yayin da Ake Ci gaba da wani aikin ceto.

Masu ibada da ‘yan uwa da masu tausayawa suna ta koke-koke yayin da ake kokarin ceto sauran wadanda abin ya rutsa da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram