Chief Ayo Adebanjo Shugaban Ƙungiyar Yarbawa ta Afenifere a jiya ya mayar wa tsohon shugaban Ƙasar Najeriya Olusegun Obasanjo martani, yana mai bayyana cewa arziƙin Man fetur na Niger Delta bana ƴan Najeriya bane.
Ya goyi bayan shugaban ƙungiyar ƴan Niger Delta Chief Edwin Clark Wanda Suka riƙa musayar kalamai da Obasanjo, akan takardar dake cewa arziƙin dake Niger Delta na ƴan Najeriya ne.
Tsohon shugaban Ƙasa Obasanjo ya taɓa bayyana cewa, ba dai-dai bane Ƙungiyar ko mutanen yankin Niger Delta su riƙa bayyana cewar arziƙin man fetur da aka gano nasu ne.
“Babu wani yanki ciki harda wanda keda wani Arziki da zai bayyana cewa nashi ne, sai dai idan an ruguza tsarin Shugaban Najeriya,” inji Obasanjo.
Dayake nashi jawabin a jiya, Adebanjo ya bayyana maganar da Obasanjo yayi a matsayin ta Son zuciya, yana mai cewa arziƙin nasu ne.