Bayan shafe tsawon watanni bakwa, Gwamnatin Tarayya ta ɗage dokar hana Twitter a Najeriya, bayan amincewa da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi.
Daraktan Kwamitin Tattaunawa da Twitter,kuma Shugaban Hukumar Kula da cigaban Fasaha ta Najeriya Kashifu Inuwa Abdullahi ya sanar da hakan.
Abdullahi a cikin sanarwar da ya fitar a Abuja, yace an bada amincewar, biyo bayan wata sanarwa da Ministan Sadarwa Prof Isa Ali Pantami ya aikewa Buhari.