Biyo bayan rabuwar auren ta, Fitacciyar Mai rawar nan ƴar Najeriya, Kafayat Shafau, da akafi sani da Kaffy, tace tana jindaɗi da auren ta ya mutu.
Kaffy wadda keda ƴaƴa guda biyu ta sanar da rabuwar auren ta da farko, tana mai cewa ta rabu da mijinta sabudda ƙaddarar su ba tazo ɗaya dashi ba.
A cikin wani bidiyo data wallafa a ranar Litinin da daddare, tace tanawa tsohon mijinta Joseph Ameh fatan abu mafi kyawu, duk da cewa sun rabu.
Datake jawabi a shafin ta na Instagram a ranar Laraba, Mai rawar nan tace ta kasance mai jindaɗi da godiya domin da ita makauniya ce, amma yanzu tana iya gani.
Kaffy tace “duk wanda suka sanni sun san cewa Ni mai rawa ce. Na maida rayuwa ta kacokan akan rawa.
“Aure na ya rabu ne saboda dalilai masu yawa, amma ina godiya saboda da Ni makauniya ce, amma yanzu ina gani.