Tsohon Gwamnan Oyo Otunba Alao-Akala, Ya Rasu

Tsohon gwamnan jihar Oyo, Otunba Christopher Alao-Akala ya rasu.

Cikakkun bayanai game da rasuwar sa na nan tafe, amma wasu majiyoyi na kusa da dan siyasar sun tabbatar wa majiyar Jaridar mu faruwar wannan mummunan lamari.

Dan siyasar wanda ya jima yana fama da rashin lafiya, ya rasu ne a gidansa dake Ogbomoso a safiyar Laraba, kamar yadda majiyoyi suka bayyana.

Wata majiya mai tushe daga jam’iyyar APC Mai Mulki, wacce ta tabbatar wa Jaridar Daily Trust rasuwar tasa a safiyar Laraba, ta ce, ya rasu ne a dakinsa.

“Gaskiya Oga ya rasu. Ya rasu ne da sanyin safiyar Laraba a dakinsa da ke Ogbomos. Yanzu muna cikin bakin ciki,” inji shi.

Akala ya kasance gwamnan jihar tsakanin shekarar 2007 zuwa 2011.

An haife shi a ranar 3 ga Yuni, 1950, a Ogbomoso da ke karamar hukumar Ogbomoso ta Arewa a jihar Oyo, Alao-Akala ya yi makarantar firamare a makarantar Osupa Baptist Day School, na garinOgbomoso kafin ya wuce makarantar Kamina Barracks Middle School, ta bataliya ta 5 a Tamale, dake kasar Ghana.

Wannan shi ne karo na uku da aka sanar da mutuwar wani fitaccen dan kabilar Ogbomosho a cikin wata guda.

A ranar 12 ga Disamba, shekarar 2021, Oba Oladunni Oyewumi, Soun of Ogbomoso, ya rasu.

A ranar 8 ga Janairu, 2022, Farfesa Taibat Danmole, diyarsa wacce Malama ce a Jami’ar Jihar Legas (LASU), ita ma ta rasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram