Akaron Farko An Sami Bullar Cutar Zazzabin Lassa A Jihar Filato

A jiya ne gwamnatin jihar Filato ta bayyana cewa ta samu bullar cutar zazzabin Lassa guda daya wadda ita ce ta farko a karamar hukumar Jos ta Arewa.

Kwamishinan lafiya na jihar Dr Nimkong Lar ne ya tabbatarwa manema labarai hakan a Jos babban birnin jihar.

Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, kwamishinan ya gargadi mazauna yankin da su guji siyan kayan abinci da ka iya harbuwa da kowace irin cuta.

Ya kuma shawarce su da su kula da muhallinsu da kuma tsaftar muhalli a wani bangare na kokarin dakile sake bullar cutar zazzabin Lassa a jihar.

“Ina so in kalubalanci mazauna yankin da su dauki tsaftar muhallin su da muhimmanci, don kiyaye kamuwa da kowace irin cuta.

“Ya kamata mu koyi rufe abin da muke ci da kyau kuma mu guji cin naman bera da naman daji. Ya kamata mutane su lura da irin abincin da suke ci saboda yawaitar yaduwar cutar a fadin kasar nan,” inji shi.

Mista Nimkong ya ce gwamnatin jihar ta shirya ta hanyar ma’aikatar lafiya don magance duk wani yanayi na rashin tabbas da ka iya haifar da zullumi, tare da tabbatar da cewa cutar da ta bulla a baya-bayan nan ba ta yadu ba.

Daga nan ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da wanke hannu da nisantar da jama’a da kuma amfani da na’urar wanke hannu a wuraren taruwar jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram