Duk Malamin Da Zai Cire Rigar Malanta Ya Sanya Ta Siyasa Mayaudari Ne – Sheikh Maqari

Fitataccen malamin addinin musulunci, Dr, Ibrahim Maqari ya ce duk malamin da ke cire rigar da ke wuyansa ta malunta ya sanya ta siyasa mayaudari ne.

Dr, Maqari ya bayyana haka ne a shafinsa na facebook a yau Alhamis.

Ya wallafa a shafin cewa, al’umma suna girmama malamai ne saboda ƙima da darajarsu ta addini.

“Yaudarar kai ne Malami ya sauya rigar wuyarsa da ta campaign, tumasanci da maula ga ƴan siyasa sannan ya zaci zai cigaba da morar wancan ƙimar da mutunci ta malanta.” In ji Dr, Maqarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram