Mafi Yawan Ƴan Najeriya Suna Farin Ciki Da Gagarumin Aikin Da Muke Yi – In Ji Shugaban Majalisar Dattawa

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya amince cewa Majalisar ta 9 da ke karkashinsa ba ta zama Gwarzuwa ba, kuma ta tafka kura-kurai.

Lawan, ya lura cewa Majalisar za ta gyara kura-kurai kafin cikar wa’adinsu.

Ya bayyana haka ne a ranar Laraba a lokacin da kungiyar ‘yan jarida ta majalisar dattawa ta kai masa ziyara domin taya shi murnar cika shekaru 63 a duniya a Abuja.

Shugaban majalisar dattawan ya ce majalisar dattawa da kuma majalisar dokokin kasar na ci gaba da jajircewa wajen biyan bukatun ‘yan Najeriya domin gudanar da ayyukansu, kamar yadda kundun tsarin mulki ya tanada.

A cewar Lawan: “Mun yi imanin cewa akwai farashin da za a biya don komai, amma muna da kishin kasa. A kira mu kowane suna, abin da muke so mu yi kuma mu cimma shi ne kasarmu ta inganta.

“Gobe, wasu daga cikin wadannan mutanen da suke kiran mu da kowane nau’in suna za su rubuta sharhi mai kyau kan abin da muka samu a wannan majalisa ta tara.

“Mafi yawan ‘yan Najeriya suna farin ciki da abin da muke yi,lj ba mu cika Dari bisa Dari ba, Kuma muna yin kura-kurai kuma za mu gyara su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram