An Buƙaci Ƴan Najeriya Da Su Zamanto Masu Son Zaman Lafiya Domin Gudanar Da Sahihin Zaɓe A 2023

Wani mai taimako kuma ɗan kasuwa Ambasada Mpakaboari Long John ya buƙaci ƴan siyasa dasu zama masu Son zaman lafiya, domin tabbatar sahihin zaɓe a Najeriya.

Mai mallakin MLJ Marine oil da Gas, ya bayyana roƙon a ranar Alhamis, inda ya buƙaci jam’iyyu da ƴan siyasa dasu guji duk wani abu da ka iya janyo rugujewar zaɓe mai zuwa.

“Munfi son mutanen daza suyi siyasa da basira. Siyasa wani ɓangare ne mai mahimmanci ga ɗan Adam. Ta hanyar siyasa shugabanni a matakai daban-daban ke isa a wasu lokuta, don haka siyasa ya kama a guji gudun yin ko ayi rai ko a mutu.

“Ku zama ƴan uwa da Allah ya halitta akan shi. Domin siyasa itace abunda za’iya cewa tana karfafa ta’addanci a ƙasa. Don haka muke buƙatar wanda zasu yi siyasa da basira da jagorancin manya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram