Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya ta gargaɗi Gwamnoni da su guji siyasantar da ilmi ta hanyar gina Jami’o’in da baza su iya ɗaukar nauyi ba.
Ƙungiyar ta bada shawarar ne a Sanarwar bayan kammala taro data bayar a ranar Juma’a, bayan taron ta na Shiyya a Maiduguri.
Takardar taron bayan kammala taron, Mataimakin Shugaban Ƙungiyar mai wakiltar shiyyar Arewa maso Gabas Abdulkadir Isa ya karanta ta.
Takardar bayan taron wadda tayi kira ga Gwamnoni dasu zuba kuɗi sosai wajen ilmi, tace bari da rashin kuɗaɗen tafiyar da Jami’o’i da wasu Gwamnoni suke yi, shiya kawo tsaiko a batun koyo da bincike wanda akwai buƙatar kai ɗauki gaggawa.
Ta kuma yi Allah wadai da sakin Naira biliyan 22.1 da Gwamnatin Tarayya tayi a matsayin kuɗaɗen alawus-alawus, inda masu koyarwa zasu samu kashi 75, a yayinda zasu samu kashi 25, inda suka yi kira da a sake dubi akan haka.
“Ƙungiyar ta bayyana damuwar ta na yadda ɓangaren waɗanda basu koyarwa a jami’ar an maida su sanuwar ware ta hanyar karya dokoki da aka gindaya na gina jami’o’i.
Ta kuma bayyana damuwar ta akan matsalar tsaro da hauhawar farashi a Ƙasa, inda tayi kira magance matsalar.