Bayan Rusa Asusun Haɗin Gwiwa Wasu Ƙananan Hukumomi Sun Shiga Halin Ƙaƙa-Nika-Yi A Neja

Wasu kananan hukumomin jihar Neja sun soma shiga halin kaka-nika-yi bayan rusa asusun hadin gwiwa, wato ‘Joint Account’ a turance da gwamnatin jihar ta yi a cikin shekarar da ta gabata.

Rusa asusun ya biyo bayan zanga-zangar da kananan hukumomin jihar suka yi a cikin watan Satumban 2021 domin nuna kin amincewarsu da asusun hadin gwiwar.

Tun ba a je ko ina ba, wasu kananan hukumomin jihar ta Neja ciki har da karamar hukumar Suleja, sun gaza biyan ma’akatansu cikakken albashi, sai dai rabi da rabi, wato sai dai ma’aikaci ya samu abin da ya sauwaka a karshen wata.

Wani mai rike da mukamin siyasa kuma jigo a karamar hukumar Suleja da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, shugaban karamar hukumar ya fada masu cewa, ma’aikatar kula da kananan humomin jihar ce ta zabtare masu kimanin nera milyan 15 a cikin watan Disamban 2021 kuma.

Hakan a cewarsa shine ya tilasta wa karamar hukumar biyan ma’aikatanta kashi 70 na albashinsu na watan na Disamba.

Sai dai a wani rahoton da muka samu, kwamishinan kananan hukumomi da masarautun jihar ta Neja, Emmanuel Umar, ya ce, ma’aikatarsa ba ta da iko dangane da kudaden kananan hukumomi, aikinsu kawai shine tabbatar da ganin kananan hukumomin na gudanar da al’amuransu daidai da tsarin doka.

Akwai bukatar ganin gwamnatin tarayyar Najeriya ta shigo domin daidaita al’amurra tare da ceto kananan hukumomin kasar ta hanyar kara daunin kudaden da take ba su idan har tana so su ci gashin kansu yadda ya kamata.

Akwai kuma ganin ana sanya wa kananan hukumomin ido sosai domin hana su almubazzaranci da kudaden jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram