Da Ɗumi-ɗumi: Masari Ya Ɗage Dokar Kasuwannin Shanu Da Gidajen Man Futur Da Aka Kulle A Jahar

Gwamnan jahar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, Aminu Masari, ya bayar da umarnin gaggauta bode kasuwannin shanu da gidajen man fetur da aka dakatar a jahar saboda matsalar tsaro.

Umarnin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jahar, Mustapha Inuwa ya sanya ma hannu a ranar Assabar ɗin nan.

Sanarwar dai ta buƙaci sarakunan Katsina da Daura da su ja kunnen hakimansu da Dagattai da masu unguwanni da su gargaɗin sarakunan fawa cewa kar su kuskura a ɓata garin mutane su haɗa kai da su wajen yin wani abu da zai sa a dawo da dokar.

In za a iya tunawa, an sanya dokar ne a watan Satumba na shekarar 2021 da ta gabata da nufin shawo kan matsalar tsaro musamman satar dabbobi da garkuwa da mutane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram