Zamu Ƙirƙiro Sabbi Dabaru Don Kawo Ƙarshen Ta’addaci A Katsina.

Gwamnan jahar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, ya ce gwamnatinsa zata ƙirƙiro sabbi dabaru wajen magance ta’addanci a faɗin jahar.

Masari, ya bayyana haka a yayin Bikin Tunawa Da Mazan Jiya wanda ya gudana a farfajiyar Katsina Peoples’ Square a yau Asabar,

Kakaki network ta ruwaito cewa, Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatin sa na ganin ta magance matsalar ta’addanci dake wanzuwa a jihar ta hanyar ƙirƙiro sabbin dabaru tareda haɗin gwiwar jami’an tsaro da kuma al’ummar jihar.

Daga bisani kuma Masari ya jinjina ma dakarun rundunar sojin ƙasar da na sama da sauran jami’an tsaro game da gudunmawarsu wajen ɗorewar zaman lafiya A Katsina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram