Mahaifiyata Ce Ta Sanya Ni In Kashe Ƙanena Domin Tsafin Neman Kuɗi -Wani Ɗan Yahoo Ya Tabbatar

Afeez Olalere mai shekaru 32 wanda Rundunar Ƴan Sandan Jahar Lagos suka kama ya tabbatar da cewa mahaifiyar shi ce ta sanya, ya kashe ƙanen shi domin tsafin neman kuɗi.

Wanda kuma ake zargin shi da damfara a yanar gizo ya kuma bayyana haka, bayan ƴan sanda sun kama shi lokacin yin binciken shi akan hanyar Itamaga, Ikorodu a Jahar Lagos.

Yace “mahaifiya ta, ta kaini ga wani Mai maganin gargajiya wanda ya gaya mani cewa idan ina so in samu nasara akan damfara a yanar gizo, to dole sai ya sadaukar da rai guda, kuma dole ya kasance ɗan uwa na jini.

Ya bayyana cewar, Mahaifiyar shi ce ta sanya ya kashe ƙanen shi mai shekaru 21, wanda ya yi haka ta hanyar sanya mashi guba.

Afeez ya bayyana cewa ƙanen shi ya mutu, mintuna 20 bayan ya sanya mashi gubar.

Ya kwashe sauran sassan jikin sa da akace ana so, a yayin da sauran aka kai shi wajen ajiye gawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram