Mata a Jihar Ondo Sun fito Zanga-Zanga Tsirara-Tsirara Saboda Rashin Tsaro

Daruruwan mata ne daga kananan hukumomi hudu na jihar Ondo, suka fito don gudanar da zanga-zanga a ranar Asabar din da ta gabata, domin nuna rashin amincewarsu da matsalar rashin tsaro a yankin.

Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da zanga-zangar lumana a garuruwan Oka Akoko, Akungba Akoko da kuma wasu yankuna a Akoko.

An ce zanga-zangar ta samo asali ne sakamakon sace malamai da wasu ‘yan ta’adda suka yi a garin Auga Akoko, da kuma kisan jami’in dan sanda da wasu ‘yan bindiga suka yi a Oka Akoko a makon jiya, da kuma harin da wasu ‘yan fashi da makami suka kai wa matafiya 17 a kan titin Ifira Akoko zuwa Isua. da sauransu.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar da ke rike da tsintsiya madaurinki daya a hannunsu, sun kasance tsirara, suna rera wakokin hadin kai iri-iri a kan tituna.

Sun yi kira ga jami’an tsaro da gwamnatin jihar da su kawo daukin gaggawar game da yadda ‘yan bindigar suka kai wa yankunan hare hare.

Da yake jawabi ga matan da suka yi zanga-zangar, Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya reshen Akoko na kananan hukumomi hudu kuma Sarkin Oka Akoko, Oba Yusuf Adeleye, ya ce kalubalen tsaro da kasar nan da jihar Ondo da yankin Akoko ke fuskanta nan ba da jimawa ba za su zama tarihi, yana mai cewa. Za a yi amfani da ƙoƙarin al’umma a matsayin hanyoyin magance matsalolin,.

Sarkin ya yi kira ga al’ummomi daban-daban a Masarautar Akoko da su “kafa kungiyoyin ‘yan banga wadanda ya kamata a karfafa mafarauta da su domin yaba kokarin hukumomin tsaro na yau da kullum.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram