Ɗan Shekara 16 ɗan fashi da makami ya bayyanawa Kotun Majistare yanda yayi fashi, ya kuma yi fyaɗe ga wasu tsofaffi a yankin Okitipupa na Jahar Ondo.
Mai Shekara 16 wanda ya bayyana cewar ya zama ɗan fashi da makami, bayan ya gudu daga Makaranta yana JSS3 , a gaban Babban Kotun Majistare domin fashi da Makami da fyaɗe.
Ya shaidawa Kotu yanda yayi fashi ya kuma yi fyaɗe ga wasu mata a ranar 24 ga watan Nuwamba na shekarar 2021, da misalin ƙarfe 12:30 a sansanin Sekere na yankin Okitipupa na Jahar.
Mai shigar da ƙarar Oluwasegun Akeredolu ya shaidawa Kotu cewa wanda ake zargin ya tabbatar dacewa ya aikata fashi da makami da kuma fyaɗe.
Yadai yiwa wata Serifat Tijani fashi saboda Naira N15,00, a lokacin yayi mata fyaɗe da makami mai hatsari.
Akeredolu wanda ya bayyana cewar, wanda ake zargin yayi ƙoƙarin keta mata haddi, bayan ya yi mata fashi, bai samu nasara ba, sakamakon taimakon wasu zuwa wurin, wanda suka taimaka mata.
Mai Shigar da Ƙara na Gwamnati ya kuma ƙara dacewa wanda ake zargin ya kuma shiga gidan wani Mewo Kolawole, inda ya sace kayan sanyawa na ƴaƴan shi.