Wani Mutum Yayi Ma ‘Yar Shekara 3 Fyaɗe A Bauchie

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wani Mutym Mai sunaAli Lawan da ke karamar hukumar Kirfi a jihar bisa zargin yi wa ‘yarsa ‘yar shekara uku fyade.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ahmad Wakil, ya fitar a jiya, ya ce matar wanda ake zargin, Mai suna Maryam Abdullahi ce ta kai rahoton lamarin wanda ya faru a ranar 9 ga watan Janairu zuwa hedikwatar ‘yan sanda na Kirfi a ranar.

Ya ce, “Wata Maryam Abdullahi mai shekaru 24 a Anguwar Doya, karamar hukumar Kirfi ta Jihar Bauchi, ta kawo rahoto a hedikwatar ‘yan sanda na Kirfi a ranar cewa mijinta Ali Lawan ya ce ta kawo masa tabarma ya kwantar.mata da yar’sa Hajara (ba sunan gaskiya ba) mai shekaru uku don ta yi barci.

“Daga baya ta dawo daki ta tarar da Hajara a kwance a sume tana ta gumi tana amai ta bakinta, hancinta, al’aurarta ta kumbura. Bayan samun rahoton ne aka tura tawagar jami’an ‘yan sanda zuwa wurin, inda aka garzaya da yarinyar zuwa babban asibitin Kirfi domin samun kulawar gaggawa. Likitoci sun tabbatar da cewa an yi mata fyade. An kama wanda ake zargin kuma ana ci gaba da bincike kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.”

Wakil ya kuma bayyana cewa a cikin wannan mako ne rundunar ta kama Wasu wadanda ake zargi da aikata fyade da kuma masu garkuwa da mutane tare da kwato harsasai, da kuma ceto wadanda aka yi garkuwa da su.

Ya ce ‘yan sandan sun kuma ceto wani Shu’aibu Abdulkarim mai shekaru 15, bayan da wani mutum mai suna Adamu Musa mai shekaru 27, dan unguwar Sabon Garin Batal dake karamar hukumar Tafawa Balewa, ya yi garkuwa da shi da kan sa, tare da ambaton wasu mutane bakwai da suka hada baki da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram