An Tsinci Gawar Wani Mutum A Otal, Batare da Wasu Sassan Jikinsa ba A Anambra.

An tsinci gawar wani mutum mai shekaru 41, Mista Azubuike Nwokolo Wanda aka Fi Sani da Zubby More a wani dakin otel da ke Amichi, na karamar hukumar Nnewi ta Arewa a jihar Anambra ba tare da wasu sassan jikinsa ba

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mahaifin ‘ya’yan biyun ya halarci liyafa ne a yankin a ranar 13 ga watan Janairu, kuma ya yanke shawarar sauka a wani otal lokacin da ya makara ya je gida sai aka ga gawarsa.

Daya daga cikin abokan marigayin, Nnaemeka Ikerionwu, wanda ya bukaci a yi masa adalci a shafukan sada zumunta, ya ce an same shi gawarsa a wani dakin otel da ke Amichi, jihar Anambra.

“Ya tafi liyafa, da dare ya yi, ba zai iya komawa gida ba, sai ya yanke shawarar sauka a wani otal a Amichi, Jihar Anambra. Bai koma gida ba wanda hakan ya sa ‘yan uwansa cikin damuwa,” inji Ikerionwu.

A cewarsa, bayan bai koma ga iyalansa ba ne suka gudanar da bincike inda suka gano cewa ya sauka a otal din.

Ya ce ko da jami’an otal din suka tabbatar ya mutu ba su tuntubi iyalansa ko ‘yan sanda ba kafin su kai shi dakin ajiye gawa.

Ikerionwu ya ce, “Wani ne da ba a san ko wanene ba ne ya sanar da iyalan cewa dansu na kwance a dakin ajiye gawa. Iyalin sun je dakin ajiye gawa ne suka gano cewa Babu yayan marenansa. Da suka tuntubi jami’an otal din, sai suka ce, ya zame a kan tayal din ban daki ne ya mutu.”

A cewarsa, ‘yan uwa da abokan arziki suna kira ga rundunar ‘yan sandan jihar Anambra da ta dauki matakin da ya dace domin ganin an yi adalci.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Toochukwu Ikenga, ya ce ba shi da masaniya kan faruwar lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram