Mai tsaron bayan Super Eagles, Chidozie Awaziem, a ranar Litinin, ya bi sahun abokan wasansa domin yin atisaye a karon farko a Garoua na kasar Kamaru.
Dan wasan bayan ya murmure daga raunin da ya ji a idon sawun.
A ranar Juma’a ce dai, koci Augustine Eguavoen, ya ce Awaziem ba zai buga karawar da suka yi da Sudan ranar Asabar ba saboda raunin da ya samu.
“Da fatan nan ba da jimawa ba, bayyana yaushe zai dawo ya fi karfina. Ina tsammanin idan ma’aikatan kiwon lafiya suna nan a yanzu za su ba shi tabbacin ko yaushe yakamata ya dawo filin wasa.
“Awaziem har yanzu yana kasa, yana da rauni a idon sawu kamar yadda na sani kuma zai dawo nan ba da jimawa ba,” in ji shi.
Amma dan wasan bayan ya yi atisaye da wasu ‘yan wasa a yau Litinin.
Babu tabbas ko zai buga wasan da za Super Eagles za tayi da Guniea-Bissau.