Baban Lauyan kuma mai rajin kare hakkin bil’adama, Cif Mike Ozekhome, SAN, ya shiga cikin sahun Lauyoyin dake aikin kare Nnamdi Kanu domin ya kara kare shi kan sabon tuhume-tuhumen ta’addanci da gwamnatin tarayya ta ke yi masa.
Ozekhome ya afkawa babbar kotun tarayya tare da Ifeanyi Ejiofor wanda a baya ya jagoranci tawagar lauyoyin Kanu.
Ejiofor ya tabbatarwa Jaridar DAILY POST cewa an samu sauye-sauye a bangaren tsaro duba da sabbin tuhume-tuhumen da gwamnatin tarayya ta yi.
A halin yanzu dai an tsaurara matakan tsaro a harabar Kotun da kewaye.
Jami’an hukumar tsaro na farin kaya, DSS sun tare duk wata hanya da ke zuwa kotun, domin dakile barazanar da ‘yan bindiga ke yi wa rayuwar mutane da kuma kayayyakin kasuwancin su