Gwamna Zulum Ya Sha Yabo Akan Dokar Da Ke Bada Kariya Ga Ƙananan Ƴara A Borno

Hukumar kula da Tallafawa kananan yara ta Dujiya, dake gudanar da harkokin ta a Najeria, ta yabawa Gwamnatin jihar Borno da Majalisar Dokokin jihar, game da amincewa da Dokar bada kariya ga yaran jihar.

Majalisar dai ta amince da gudurin ne a watan Disambar 2021, da gwamnan jihar ya rattabawa hannu ta zama doka a ranar 10 ga watan janairu da muke ciki.

Dokar dai na bukatar samar da kariya ga yaran da suka kwashe tsawan shekaru 12,suna fuskantar rikici a yankin.

Ku dokar zata cigaba da Inganta tare da bada kariya ga yaran.

A Tsokacin ta, Daraktan Hukumar a Najeria, Mercy Gichuli, tace amincewa da Dokar a sabuwar Shekara, tamkar kyauta ce ga yaran jihar Borno, dake da Gwamnati mai tausayi da jin koken yaran da suka kwashe tsawan shekaru suna bukatar kare musu rayukansu.

Shugaban Majalisar Yara ta jihar Borno, Ibrahim Zanna Sunoma, yace Majalisar ta bayyana godiyar ta game da wannan hubbasan ga daukacin masu ruwa da tsaki da suka bada gudunmawa wajan ganin an kafa dokar.

Kazalika ya kuma Godewa Gwamnatin jihar na samar da kudurin da sanya mishi hannu ya zama doka, yana fatan ganin dokar tayi tasiri ta yadda ya kamata a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram