Gwamnoni Sun Daina Almubazzaranci Da Dukiyar Ƙasa A Yanzu – In Ji Gwamna Badaru

Gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Badaru Abubakar, ya bayyana cewa Gwamnonin Najeriya yanzu sun rage
almubazzarancin da suke a baya na ‘ban natar da kudaden gwamnati.

A cewar shi, Gwamnoni yanzu sun daina yawo cikin motoci sama da 30 kamar yadda suka saba,
bayyana hakan ne a hirarsa da kafar Talabijn ta Channels a daren ranar litinin.

Yace shi da takwarorinsa Gwamnoni, na iyakan kokari wajen rage kudaden da suke kashewa na gudanar da harkokin ofishohinsu.

Gwamnan, yace yanzu Takwarorinsa, kawo yanzu sun maida hankali wajan daukan ma’aikata a sashen Ilimi da kiwon lafiya da sauran wasu mahimman ayyukan ci gaban kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram