Dan Wasan Arsenal Kolasinac Ya Koma Marseille

Dan wasan bayan Bosnia da Herzegovina na Arsenal Sead Kolasinac ya koma Marseille kan kwantiragin watanni 18, in ji kulob din Faransa a ranar Talata.

Kolasinac, mai shekara 28, ya rattaba hannu kan kwantiragi har zuwa watan Yuni 2023 bayan ya bar Emirates, tare da kawo karshen yarjejeniyarsa “bisa amincewar juna”, in ji Gunners a cikin sanarwar nasu.

Ya lashe kofin FA sau daya da Community Shield sau biyu tun da ya isa arewacin Landan daga Schalke a shekarar 2017.

Dan wasan ya shafe watanni shida a kakar wasan da ta gabata a matsayin aro a kungiyar ta Jamus kuma ya buga wa Gunners din wasanni mintuna 270 kacal a wannan kakar.

Ya zama dan wasa na biyu da Marseille ta dauko a watan Janairu bayan dan wasan DR Congo Cedric Bakambu ya koma Kungiyar a makon jiya kuma za a gabatar da shi ga manema labarai a gobe Alhamis.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram