A zaɓe mai zuwa na 2023 jam’iyyar PDP ce zata ɗare saman duk manyar kujerun siyasa – Dr, Garba Shehu Matazu.
Wakilin kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP Dr Garba Matazu ya bayyana cewa suna kyautata zaton jam’iyyar su ce zata ɗare saman manyan kujeru a zaɓe mai zuwa a shekarar 2023.
Dr, Matazu ya bayyana haka ne a yayin da ya ke ganawa da manema labarai a gidanshi a ranar Talatar nan.
Matazu ya ƙara da cewa, duk da jam’iyyar APC ke mulki amma kuma da ka ga yayan jam’iyyar kasan suna cikin halin kunci da rashi.