A yammacin Larabar da ta gabata ne masu tuka babur da gwamnatin jihar Kano suka cimma yarjejeniya kan harajin rajistar sabbin kKeke Napep da sabunta lasisi tukin su
’Yan kasuwa masu sana’a a jihar sun shiga yajin aikin kwanaki uku a makon da ya gabata don nuna adawa da sabon harajin.
Yarjejeniyar ta samu jagorancin kungiyar lauyoyin Najeriya a Kano a wani taro da ya dauki tsawon awanni shida ana gudanar da shi wanda ya samu halartar hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano KAROTA da masu tuka Babura Mai kafa Uku da wakilansu na lauyoyi.
A Taron an yanke shawarar rage kudin daga N8,000 zuwa N5,000 don sabuntawa da kuma N12,000 na rajista daga N18,000, wanda za a biya tsakanin watan Janairu zuwa karshen Fabrairu.
Darakta na KAROTA, Baffa Babba Danagundi, ya ce rashin biyansu a cikin wa’adin da aka amince da shi zai sa a biya N18,000 da ta gabata na sabon rajista da kuma N8,000 don sabuntawa.
A baya dai Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, Masu Adai-daita sahun sun dakatar da yajin aikin ne domin a samu damar tattaunawa da gwamnatin jihar.
Lauyan masu kera keken Napep, Abba Hikima, ya ce an dakatar da yajin aikin ne bayan yarjejeniyar da gwamnati ta yi na cewa za a rage harajin.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a cikin kasa da watanni 12, wannan shi ne karo na biyu da masu tuka keken ke yiwa gwamnatin Kano bore, inda matafiya suka Sha bakar wahala a lokacin yajin aiki .