Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles, za ta kece raini da takwararta ta kasar Tunisia a zagayen gaba na gasar cin kofin kasashen Afirka, wato AFCON 2021, wanda ke gudana a kasar Kamaru.
Najeriya ta kammala wasanninta a rukunin D da maki 9 bayan cinye dukkanin wasanni 3 da ta buga wanda kuma ya sanya ta zama ta 1 a rukunin.
Labarin da muka samu daga jaridar ‘Punch’ ya bayyana cewa, kasar Masar wadda ta zo ta 2 a rukunin da maki 6, za ta hadu da kasar Ivory Coast a zagaye na biyun inda kasashe 16 za su fafata.
Ga dai yadda aka hada kasashen a zagayen na gaba wanda za a soma a ranar Lahadi, 23 ga watan Janairu, 2022, ranar da Najeriya za ta yi wasanta da Tunisia.
Lahadi, Jan 23
Burkina Faso v Gabon, Limbe, 16:00
Nigeria v Tunisia, Garoua, 19:00
Litinin, Jan 24
Guinea v Gambia, Bafoussam, 16:00
Cameroon v Comoros, Yaounde (Olembe), 19:00
Talata, Jan 25
Senegal v Cape Verde, Bafoussam, 16:00
Morocco v Malawi, Yaounde (Ahmadou Ahidjo), 19:00
Laraba, Jan 26
Ivory Coast v Masar, Douala, 16:00
Mali v Equatorial Guinea, Limbe, 19:00
Za a yi wasannin Dab da na kusa da na karshe, wato ‘Quarter Final’ a ranakun Asabar, 29 da Lahadi, 30 ga watan Janairu.
Wasannin kusa da na karshe, ‘Semi Final’ kuma, za a buga su a ranakun Laraba, 2 da Alhamis, 3 ga watan Fabrairu.
Wasan da kasashe 2 da aka mako daga wasannin kusa da na karshe za su buga domin neman na uku a tsakaninsu wanda za a yi a ranar Lahadi, 6 ga watan Fabrairu da misalin karfe 4pm.
Sai kuma wasan karshe wanda shi ma za a buga shi a ranar Lahadin, 6 ga watan Fabrairu da misalin karfe 7pm.
Najeriya dai wadda ta lashe kofin na Afirka sau 3, ana yi mata kallon daya daga cikin kasashen da za su dauki kofin a wannan karo ta la’akari da yadda take taka leda da kuma zaratan ‘yan wasan da Super Eagles din ke da su.