Shigen Yadda Akai Ma Hanifa: An Sake Tsintar Gawar Wani Yaro Dan Shekara 3

Wani yaro mai suna Aminu Bukar dan shekara uku da ya bace a karamar hukumar Guri ta jihar Jigawa a makon jiya, an tsinci gawarsa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Lawan Shiisu ne, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce tun da farko mahaifin yaron Alhaji Bukar ya kai wa ‘yan sanda rahoton cewa yaron nasa ya bace da misalin karfe 4:00 na yamma a kauyen Dolen Zugu a ranar 14 ga watan Janairun 2022.

Ya ce, a lokacin da aka samu rahoton, tawagar ‘yan sanda ta zage damtse, inda daga bisani suka gano gawar Aminu a dajin Tudun Mai Jambo, kimanin kilomita daya daga kauyen.

PPRO ya ce an garzaya da Aminu asibiti kuma likita ne ya tabbatar da mutuwarsa.

Ya ce binciken da ‘yan sanda suka gudanar ya tabbatar da cewa babu wani mugun wasa a cikin mutuwar yaron.

Shiisu ya kara da cewa daga baya an dawo da gawar ga ’yan uwa domin yi masa jana’iza.

Wannan mummunan lamari dai ya zo ne a daidai lokacin da ake nuna bacin rai kan yadda aka yi garkuwa da Hanifa Abubakar, wata yarinya ‘yar shekara biyar da haihuwa a Kano.

Dangane da Hanifa, Abdulmalik Tanko, mamallakin makarantar da ta zuwa, ya amsa laifin kashe ta da gubar bera.

An kama shi ne bayan karbar wani bangare na kudin fansa Naira miliyan 6 da ya nema daga iyayen yarinyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram