Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya gargaɗi magoya bayan sa akan zagin Jigon Jam’iyyar APC na Ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Kuma tsohon Gwamnan Jahar Lagos, a yayinda dukkanin su idanuwan su na akan samun takarar shugabancin Najeriya a shekarar 2023.
A yayinda dukkanin su ke neman tikitin Jam’iyyar na tsayawa takara, wasu magoya bayan Tinubu sun fara caccaki Osinbajo na ƙin goyon bayan takarar shugaban Ƙasa na Tinubu duk da irin abubuwan da yayi mashi a harkar siyasa.
A cewar Jaridar Vanguard, wani Makusancin Osinbajo ya ce mataimakin shugaban Ƙasa yana gargaɗin kowa akan zagin Tinubu, kuma ya gargaɗi magoya bayansa “koda sun zagi mahaifiya ta kada ku rama. Babu wani dalili da zai sa ku zage shi.
Haka zalika, magoya bayan Osinbajo a yankin Arewa sune Sarakuna, wanda suke ganin Osinbajo a matsayin wanda yayi biyayya ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Baya ga Sarakuna, Gwamnoni guda 4, biyu daga yankin Arewa maso Yamma, da guda biyu a yankin Arewa maso Tsakiya, suma suna goyon bayan Mataimakin Shugaban Ƙasa. Amma Tinubu yafi yawan jama’a a yankin Arewa.