Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ƴan wasan Super Eagles na Najeriya da su cigaba da ƙwazon da suke yi a gasar cin kofin Nahiyar Afirka da ake gudanar wa a halin yanzu.
Buhari yayi wannan kiran ne a ganawar da yayi da ƴan wasan ta hanyar bidiyo, gabanin fara fafatawa kashi na biyu da Tunisia a daren yau.
Super Eagles dai zata fafata da Ƙungiyar wasa ta Tunisia a filin wasa na Roumdé Adjia dake Garoua na ƙasar Cameroon, da misalin ƙarfe 8 na dare a ranar Lahadi.
Dayake jawabi a taron da yayi da ƴan wasan ta kafar yanar gizo ta hanyar bidiyo a fadar shugaban ƙasa dake Villa, Abuja, Shugaban Ƙasar yayi jawabi ne da Kocin Augustine Eguavoen, da Kaftin Ahmed Musa, da Amaju Pinnick, da Shugaban Hukumar Kula da Ƙwallon Ƙafa, da Wakilin Najeriya a Ƙasar Kamaru, Janar Abayomi Olonisakin (mai ritaya).
Dayake kiran sunan ƴan wasa guda biyu Kelechi Iheanacho da Moses Simon a suna, Buhari ya buƙaci Super Eagles da su cigaba da sanya ƴan Najeriya cikin murna, bawai wajen samun nasara kaɗai ba, har da ɗaukar Kofin.
“Kuna sanya Najeriya alfahari, kuna samun nasara. Ku cigaba da samun nasara. Gwamnatin Tarayya na goyon bayan ku, kuma ina godiya ga dukkanin ƴan wasan. Ku cigaba da sanya Najeriya alfahari,” Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa Femi Adesina ya naƙalto Shugaba Buhari na faɗa.
A cewar Adesina, Shugaban Ƙasar ya kuma yabawa kyakkyawan aikin Ministan Wasanni da Cigaban Matasa Sunday Dare, inda yace Ƙasar na jinjinawa da hakan.