Akalla Mutane 7 Ne Suka Mutu Sakamakon Harin Bam Da Aka Kai A Herat Na Afganistan

Wani harin bam da aka kai kan wata karamar motar bas a garin Herat da ke yammacin Afghanistan ya kashe mutane akalla bakwai tare da jikkata wasu da dama, a cewar hukumomin yankin.

An kai harin ne a kusa da tashar mota a yankin da ‘yan tsiraru ‘yan Shi’a Hazara ke zaune a birni na uku mafi girma a kasar a ranar Asabar. An makala wani bam mai danko a tankin mai na motar kafin fashewar. Lamarin da kuma ya Kai ga jikkata mutane tara.

Arif Jalali, shugaban asibitin lardin Herat ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, “mata hudu na daga cikin bakwai da suka mutu.”

Sabit Harwi mai magana da yawun ofishin leken asiri na Herat shi ma ya tabbatar da tashin bam din. Inda ya ce, “Rahotanni na farko sun nuna cewa bam ne da ke makale da tankin mai na motar fasinja ya fashe.”

Yan sandan lardin Herat da ma’aikatar al’adu su ma sun tabbatar da tashin bam din.

Ya zuwa yanzu dai babu wani mutum ko wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, amma jami’an Taliban a baya sun zargi kungiyar ta’addanci ta Daesh da kai irin wadannan hare-hare kan fararen hula.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram