Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Tirela Da Keke Napep A Kano

Wani Jirgin Ƙasa ɗauke da matafiya ya murƙushe Tirelar Simunti ta Ɗangote da Kuma Keke Napep a Kano.

Lamarin ya faru ne a hanyar Obasanjo dake cikin birnin Kano a ranar Asabar da safe.

Wani wanda ya shaida lamarin, da ya kasance yana sana’a kusa da hanyar Jirgin Ƙasa, yace yaga Tirela na tahowa zuwa hanyar Jirgin a lokacin da Jirgin Ƙasa ke kan hanyar shi yana gudu.

Ya ƙara dacewa sun so suyi ƙoƙarin saukar da Tirelar, amma Direban bai lura ba.

Har yanzu babu takamaiman rahoto cewa ko an kashe mutum, amma mutane sun nufi Asibitin Murtala Muhammad daga wurin da hatsarin ya faru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram