Ƙaramin Ministan Man Fetur Timipre Sylva yace Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yace Shugaban Ƙasa baya goyon bayan cire tallafin Man Fetur.
Sylva ya bayyana haka a lokacin da ya bayyana a shirin Newsnight na gidan Talabijin na Channels.
“Zan gaya maku a wannan lokacin cewa, cire tallafin mai gaba ɗaya bashi ne ke gaban mu ba.
“Shugaban Ƙasar Najeriya baya goyon bayan cire tallafin man fetur a wannan lokacin,” inji shi.
Ministan ya bayyana cewar daga cikin dalilan da suka sanya Gwamnatin Tarayya bata tunanin cire tallafin man fetur saboda abinda zai haifar ga ƴan Najeriya.
“Yace ” wannan abune dake buƙatar yin aiki tsakanin Gwamnatin Tarayya da Jahohi, saboda abinda ya shafi ƙasa ne. Muna aiki da Gwamnoni a halin yanzu.