Rahotanni daga jihar Kano da ke Arewa maso gabashin Najeriya na cewa wata Kotun Majistare a jihar ta tsare malamin nan da ya amsa laifinsa na kisan ɗalibarsa ƴar shekara biyar, wato Hanifa Abubakar tareda wasu mutane biyu da ake zargin sun taimaka masa.
Kakaki Network ta ruwaito cewa an gurfanar da Abdulmalik Tanko da Hashimu Isyaku da Fatima Musa a gaban kotun bisa zargin haɗa kai wajen aiwatar da laifin garkuwa da mutane, da cin amana da zamba cikin aminci da kisan kai wanda hakan ya ci karo da dokar sashe na 97, 274, 277 da kuma sashe na 221 na manyan laifukka.
A yayin gudanar da Shari’ar karo na farko, Attorney General
kuma Kwamishinan Shari’a na jihar Kano, Musa Lawan ya roƙi kotun da ta ba masu shigarda ƙara wa’adin sati ɗaya domin su samu zarafin yin nazari tareda shirya tuhume tuhumen da za su yiwa waɗanda ake ƙarar.
Kazalika ya roƙi kotun da ta ajiye waɗanda ake zargin a gidan gyaran hali.
Daga bisani, Alƙali mai Shari’a, Mahmud Jibrin ya amince da rokon a inda ya ɗage zaman sauraren shari’ar har sai ranar biyu ga watan Fabrairun wannan shekara.