Sojoji Sun Dakile Wani Hari Da Aka Kai A Birnin Gusau

Rahotanni daga birnin Gusau, na jihar Zamfara, sun tabbatar da cewa, an sace wani dan siyasar jihar Aminu Adamu a gidan sa da ke kwatas din Mareri da ke birnin.

Adamu wanda aka fi sani da Papa, shi ne manajan daraktan hukumar sufuri ta jihar Zamfara kuma makusancin Gwamna
Bello Matawalle.

Wani mazaunin yankin Zayyanu Muhammad, ya sanar da cewa ‘yan ta’addan sun bayyana ne a babura, inda kai tsaye suka tunkari kwatas din, gidan Adamu da iyalansa su ke.

Zayyanu yana mai cewa, ba Papa suka je sacewa ba, Barista Hafiz Sufyan suka je dauka amma ba ya gida, da misalin karfe 12 da rabi na dare, da shigan su gidan Papa, suka fara tambayar inda makwabcin sa Barista Hafizu ya ke, yace musu baya gari, suka ce mishi an tabbatar musu ya na
gida.

Yace Daga nan suka dauke shi da iyalansa, daga nan ne jama’ar yankin suka sanar da jami’an tsaron da ke yankin wadanda suka fuskancin ‘yan ta’addan.

Muhammad ya kara da cewa, ‘yan sa kan sun bi ‘yan ta’addan har wajen kwatas din, lamarin da ya tirsasa su sakin matan
dan siyasan biyu da yaransa amma suka tafi da shi.

An kashe ‘yan bindiga masu yawa har da wata mace a ciki, inda aka kaisu cibiyar lafiya ta tarayya dake Gusau.

Sojojin sun ceto Adamu da wani mutun guda, sai dai an harbe shi har sau biyu amma sun kai shi asibiti.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram