Wani Mai Gadin Polytechnic Ya Harbe Manomi Har Lahira

Wani mai gadi da yake aiki da Polytechnic ta Jahar Osun Iree ya harbe wani Manomie a Eripa, Ƙaramar Hukumar Boluwaduro ta Jahar.

Lamarin ya faru a cikin karshen hutu a yankin Odo-Ada dake a cikin garin.

Majiyar mu tace wanda ake zargin yayi kisan, ya shiga gona tare da satar doya daga gonar mutumen, inda a tunanin sa mai gonar ya tafi gida.

A lokacin daya lura cewa, mai gonar yana cikin ta da abokanan sa, ya buƙace su dasu tafi gida.

To sai dai bayan sun tafi gida, sai manomin ya lura dacewa ya manta wasu abubuwa a gonar, wanda ya sanya ya koma gonar, amma yana zuwa sai ya tarar mai gadin na satar mashi kayan amfanin gona.

Manomin wanda yana tare da ƴan uwan sa, ya ƙalubalanci wanda yake tonar mashi kayayyakin amfanin gona, inda anan take ya harbe shi ya gudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram