An Gurfanar Da Wani Dilan Mota Sakamakon Cin Naman Ƙaramin Yaro A Zamfara

An gurfanar da wani Dilan Mota sakamakon cin Naman Ƙaramin yaro a Zamfara

Wani Fitaccen dillalin Mota a Gusau, Babban Birnin Jahar Zamfara da wasu mutane 4 a ranar Talata an gurfanar dasu, a gaban Babban Majistare da laifin kisa, tare da cin naman ƙaramin yaro mai shekaru 9 da ake kira da Ahmad Yakubu Aliyu.

Masu laifin dai an kawo su Kotu tare da tsatstsauran tsaro.

Majistare Sa’adu Gurbin Bore ya karanta laifukan da ake zargin su, inda suka bayyana cewa basu da laifi.

Mai Shari’ar ya ɗage Shari’ar zuwa 8 ga watan Fabrairun shekarar 2022.

Tunda Farko, iyayen yaran da masu tausaya masu, sun cika kotun domin nema adalci ga ɗan su da ake kashewa.

Sun ce sun damu matuƙa da kisan, kuma bazasu yafewa wanda ya aikata laifin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram